Isa ga babban shafi

Hasashen tsawon rai ga Faransawa ne ya tilasta kara shekarun ritaya- Macron

Shugaba Emmanuel Macron na Faransa ya kare matakinsa na yiwa dokar fansho garambawul wanda zai bayar da damar karin shekarun ritaya daga 62 zuwa 64, ya na mai bayyana shirin a matsayin wata babbar kadara ga Faransawan. 

Hasashen baya-bayan nan dai na nuna cewa Faransawa za su samu karin tsawon rai a ban kasa dalili kenan da shugaban ke ganin wajibi ne a kara shekarun da za su rika shafewa suna aiki.
Hasashen baya-bayan nan dai na nuna cewa Faransawa za su samu karin tsawon rai a ban kasa dalili kenan da shugaban ke ganin wajibi ne a kara shekarun da za su rika shafewa suna aiki. REUTERS - WOLFGANG RATTAY
Talla

Wata kuri’ar jin ra’ayin jama’a ta bayyana cewa kaso mai yawa na Faransawa da kuma dukkanin mambobin majalisar kasar na jam’iyyar masu tsattsauran ra’ayi na sukar shirin na Macron wanda ke ci gaba da ganin boren jama’a ta hanyar mabanbantan zanga-zanga baya ga yajin aiki a sassan kasar. 

Macron a jawabinsa na jiya talata, wanda ke zuwa bayan daukar lokaci yana kaucewa haduwa da wakilcin kungiyoyin kwadago ya bayyana cewa daukar matakin ya zama wajibi lura da hasashen samun karuwar tsawon rai ga Faransa, wanda ken una ta wannan hanyar ne kadai za a ci gaba da tafiyar da al’amura dai dai a kasar. 

A cewar Macron sam bai kamata a jira mu’ujiza ba kamata ya yi a yi shirin tunkarar kalubalen da ke tattare da yawan tsawon ran Faransawa za su gani a nan gaba wajen tabbatar da cewa hakan bai zame musu matsala ba. 

Shugaban na Faransa wanda sam bai ambata shirin daukar irin wannan mataki ba yayin yakin neman zabensa a bara, ya shaidawa manema labarai yau a birnin Paris cewa idan har mutane suka amince da kara akalla shekaru 2 a aikinsu hakan zai taimaka wajen dakile matsalar tattalin arziki a kasar. 

Jaridun Faransa sun ruwaito Macron na cewa idan har bamu samar da kudade ba bai kamata mu rabar da shi ba, domin hakan ne zai kange kasar daga fuskantar gibin tattalin arziki nan da shekarar 2023. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.