Isa ga babban shafi

Harin Rasha ya katse lantarki a cibiyar nukiliya ta Zaporizhzhia

Masu gudanar da cibiyar samar da makamashin nukiliya ta Zaporizhzhia sun ce harin da Rasha ta kaiwa cibiyar a alhamis din nan, ya sanya su komawa yin amfani da na’urar janareta don samar da wutar lantarki a cikin ta.

Cibiyar samar da makamashi ta Zaporíjia.
Cibiyar samar da makamashi ta Zaporíjia. REUTERS - ALEXANDER ERMOCHENKO
Talla

Lamarin ya biyo bayan hare-haren da Rasha ta kai Ukraine Wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane 9 da kuma daukewar wutar lantarki a fadin kasar.

Jami’an sun ce wannan ne karo na shida da cibiyar ke fuskantar katsewar wutar lantarki, tun bayan da Rasha ta kwace ikon ta a shekarar da ta gabata.

A cewar su, janaretan da ake amfani da su wajen samar da wuta a cibiyar, na da karfin iya bada wutar lantarki na kwana 10 ne kadai.

Hukumomin Rasha da ke kulada cibiyar sun ce an kashe na’urorin janaretan ne, kuma ba su bada wani cikakken bayani ba akai.

A ranar 4 ga watan Maris na shekarar da ta gabata ne, sojojin Moscow su ka kwace ikon cibiyar, kwanaki kadan bayan kaddamar da mamayar ta a Ukraine.

Bangarorin Moscow da Kyiv na zargin juna da kai hare-hare cibiyar samar da makamashi ta Zaporizhzhia, wacce ita ce mafi girma a Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.