Isa ga babban shafi

Faransawa sun sake fitowa zanga-zangar fansho

Dubban mutane ne suka fito kan tituna a fadin Faransa a wannan Alhamis domin nuna adawa da sauye-sauyen da shugaba Emmanuel Macron ya yi na fansho, yayin da ake dakon shugaban zai sanya hannu kan sabuwar dokar. 

Jami'an tsaro na artabu da masu zanga-zanga a Faransa
Jami'an tsaro na artabu da masu zanga-zanga a Faransa AFP - LOIC VENANCE
Talla

Kamar dai yadda aka saba yi a kwanakin baya, an yi ta cece-ku-ce tsakanin 'yan sanda da masu zanga-zangar a fadin kasar, yayin da masu zanga-zangar kuma suka mamaye hedikwatar kamfanin kayayyakin alfarma na Faransa LVMH da ke birnin Paris. 

A ranar Juma’a ne ake ganin hankula za su karkata ga majalisar tsarin mulkin kasar Faransa, wadda ta kasance babbar hukumar gudanarwar kasar, wadda za ta sanar da matakin karshe kan dokar fansho a matakin karshe kafin Macron ya sanya hannu kan dokar. 

'Yan sanda na sa ran kusan mutane 400,000 zuwa 600,000 za su shiga zanga-zangar. Hakan zai kasance kasa da rabin kusan miliyan 1.3 da suka yi zanga-zanga a watan Maris a daidai lokacin da ake gudanar da zanga-zangar adawa da sauye-sauyen, wanda ya hada da kara shekarun ritaya daga 62 zuwa 64. 

Jami'an tsaro na cikin shirin-ko-ta-kwana, inda ake sa ran masu zanga-zangar kin jinin gwamnati 1,500 da masu tsattsauran ra'ayi a birnin Paris za su yi fitar dango, yayin da ake sake ganin garuruwan yankin kamar Nantes da Rennes na iya fuskantar tarzoma. 

Idan har aka amince da dokar, abin jira a gani shi ne ko kungiyoyin kwadago za su tsawaita yajin aikin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.