Isa ga babban shafi

Shugaban kamfanin Wagner ya koka da mutuwar dubban dakarun Rasha a Ukraine

Shugaban kamfanin sojojin haya na Wagner Yevgeny Prigozhin ya yi barazanar janye dakarunsa daga birnin Bakhmut, inda yaki ya fi yin Kamari a gwabzawar da ake tsakanin Rasha da Ukraine, a wata caccaka ta basa-banban, wadda ya yi wa manyan hafsoshin sojin Rasha.

Shugaban kamfanin sojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin.
Shugaban kamfanin sojin hayar Rasha na Wagner, Yevgeny Prigozhin. © Reuters 视频截图
Talla

A wasu jerin hotunan bidiyo da ya watsa ta shafi Telegram, Prigozhin ya caccaki ministan tsaron Rasha, Sergei Shoigu da babban hafsan hafsoshin sojin kasar, Valery Gerasimov a game da mutuwar dubban sojin Rasha a Ukraine, baya ga da dama da suka ji rauni.

Ya sha alwashin neman  ba’asi daga gare su a kan abin ya kira gazawarsu wajen samar wa dakarunsa isassun makamai.

Ya ce halin rashin kwarewar da suke nunawa yana halaka dubban sojojin Rasha, kuma wannan abu ne da ba za a lamunta ba.

Wagner ce ta ja ragamar yakin da aka shafe watanni ana gwabzawa a birnin Bakhmut, inda saura kiris ta karbe birnin a yaki mafi tsawo da muni tun da Rasha ta fara mamayar Ukraine.

Ko da yake  Prigozhin ya sha yin irin wannan barazana na janye dakarunsa a baya, caccaka  da ya yi wa wasu hafsoshin soji abu ne da ba a saba ji ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.