Isa ga babban shafi

Macron ya ce akwai ababen lura da su ka biyo bayan kisan matashi Nahel

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci mukarraban gwamnatin sa, su dauki darasi kan mummunar zanga-zangar da ta faru a kasar bayan kisan da ‘yan sanda suka yiwa matashi Nahel. 

Shugana Emmanuel Macron na Faransa, a lokacin da ya ke yiwa majalisar zartarsa jawabi.
Shugana Emmanuel Macron na Faransa, a lokacin da ya ke yiwa majalisar zartarsa jawabi. AFP - CHRISTOPHE ENA
Talla

Da yake yiwa sabuwar majalisar zartaswar da ya yi wa kwaskwarima a yau juma’a jawabi, Emmanuel Macron ya ce wannan zanga-zanga ta nuna irin barnar da mutane zasu iya yi idan suka fusata, da kuma irin rashin hadin kan da ake da shi a Faransa. 

Macron ya ce tarzomar da ta biyo bayan kisan matashin ta nuna bukatar da ke akwai na tilasta girmamawa da kuma mutunta juna tsakanin fararen hula da jami’an tsaro. 

Akwai tambayoyi da dama da ya zama dole mu amsa su a matsayinmu na jagorori ga al’ummar Faransa, don haka ne kadai zai wanke mu a idanun jama’a, inji mista Macron. 

Wannan tarzoma dai, itace irin ta ta farko mafi muni da ta biyo bayan wadda ta faru a 2005 da ta faru kan batun bakin haure da kuma nuna wariyar launin fata da irin cin zarafin da jami’an tsaro ke yiwa jama’a. 

Baya ga wannan kuma, shugaba Macron ya bukaci sabuwar majalisar zartaswar ta bashi goyon bayan wajen mayar da kasar kan turbar tattalin arzikin da ta sauka daga kai tun bayan cutar Corona. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.