Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda ba zasu taba nasara a Turkiyya ba-Erdogan

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayeeb Erdogan ya  ce 'yan ta'adda ba zasu taba nasara a kasar ba, dai-dai lokacin da kasashen duniya suka fara bayyana alhinin su ga kasar a sakamakon harin ta’addancin da wasu mutanen suka kai cikin ma’aikatar harkokin cikin gida dake kasar.

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyeb Erdogan
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyeb Erdogan © Анадолу
Talla

Faya-fayan bidiyon da ke yawo a kafafen yada labarai sun nuna yadda dan ta’addar ya fito daga cikin wata mota nan take kuma ya shiga cikin ma’aikatar a guje, sai dai kafin ya kai ga karasawa bam din ya tashi da shi.

Bayanai sun ce bayan maharin da ya mutu ba’a sami asarar rai ba sai jami’an ‘yan sanda guda biyu da suka jikkata.

Rabon da birnin Ankara ya gamu da harin ta’addanci tun 2016.

Ministan harkokin cikin gidan kasar Ali Yerlikaya a wani sako da ya wallafa a shafin sa na X ya ce maharan su biyu ne suka isa ma’aikatar sai dai jami’an tsaro sun yi nasarar harbe daya daga cikin su kafin ya kai ga tayar da bam din da ke jikin sa.

Har yanzu dai babu wata kungiya data dauki alhakin kai harin da ke zama tamkar sabon abu a kasar.

A jawabin da ya gudanar bayan kai harin, shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan ya yi kira ga ‘yan ta’addda da su sa a ransu cewa Turkiyya ba kasar da zasu iya ci da yaki bace.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.