Isa ga babban shafi

EU za ta sauya dokar karbar 'yan ci rani a kasashenta

Kungiyar Tarayyar Turai EU, ta cimma matsaya ta karshe na yin garambawul ga dokokin yadda za su tafiyar da sha’anin masu neman mafaka da bakin haure da ke ketarawa nahiyar ba bisa ka’ida ba, inda a yanzu kungiyar ta maida hankali don ganin matsayar da suka cimma ta zama doka a shekara mai zuwa. 

Wasu bakin haure masu neman shiga kasasahen Turai.
Wasu bakin haure masu neman shiga kasasahen Turai. REUTERS - YARA NARDI
Talla

Wakilan kasashe mambobin kungiyar 27 ne suka cimma matsayar a Brussels, bayan kasashen Italiya da Jamus sun warware takaddamar da ta barke kan kungiyoyin agaji da ke gudanar da aikin ceto bakin haure da suka makale a tekun Mediterranean. 

Ministan Harkokin Cikin Gida na Spain Fernando Grande-Marlaska, wanda kasarsa ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar ta EU, ya bayyana matsayar da suka cimma a matsayin gagarumin ci gaba kan makomar kungiyar EU. 

Mataimakin Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Margaritis Schinas, ya bayyana matsayar a matsayin hadin kai na karshe da aka rasa a baya, tare da yin kira ga kasashen mambobin EU su ci gaba da tattaunawa don samar da doka a kai. 

Burin kungiyar ta EU dai shi ne a samar da sauye-sauyen da suka kamata, gabanin zaben kungiyar da za a gudanar a watan Yunin shekara mai zuwa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.