Sama da mutane dubu 250 sun yi zanga-zangar adawa da masu ra'ayin mazan jiya a Jamus
Kimanin mutane dubu dari 2 da 50 ne suka fito zanga-zanga a fadin Jamus a jiya Asabar don nuna rashin amincewa take-taken jaam’iyya mai ra’ayin mazan jiya na AFD, wadda ta janyo cece-kuce bayan da aka samu bayanan da ke nuni da cewa mambobinta sun tattauna shirin tisa keyar baki a wani taro na masu tsatsauran ra’ayi.
Wallafawa ranar:
Dubban mutane ne suka fito a biranen Frankfurt, Hanover da Dortmund, suna daga kwalayen da ke dauke da rubutun nuna adawa da jam’iyyar ADF.
Tun daga ranar Juma’a aka yi kiran zanga-zanga a wurare dabam -dabam har dari a fadin kasar Jamus, ciki har da birnin Berlin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu