Isa ga babban shafi
FIFA

Yau ne FIFA zata zabi Gwarzon dan wasan Duniya

A yau litinin ne hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA zata zabi gwarzon dan wasan duniya tsakanin Messi da Andres Iniesta da Xavi Hanendez dukkaninsu daga kungiyar kwallon kafa ta Barcelona.Wannan dai shi ne karo na uku a tarihin kyautar gwarzon dan wasan duniya inda aka samu ‘yan wasa uku a karshe dukkaninsu daga kungiyar kwallon kafa daya tun ‘yan wasan AC Milan a shekarar 1988 da 1989 inda dan wasa Marcon van Basten ya lashe kyautar a shekarun biyu.Tuni dai jaridar Gazzetta dello ta kasar Italiya tayi hasashen cewa Andres Ineista ne zai lashe kyautar wanda ya zira kwallon karshen da ya bai wa kasar Spaniya damar lashe gasar cin kofin duniya a kasar Africa ta kudu. Sai dai shugaban UEFA Michel Platini yace Xavi Hanandez ne zai lashe kyautar, duk da cewa shugaban ya kalubalanci rashin ganin dan wasan kasar Holland Wesley Snwiejder daga cikin mutane uku da ke neman kyautar.Messi wanda shi ne gwarzon dan wasan Duniya a shekarar bara, yace gurinsa shi ne Inesta ko Xavi su lashe kyautar domin duk abinda ya zama a kwallon kafa da taimakonsu ya samu hakan. Duk da dai cewa Messi ya taka rawar gani a kakar wasan bara kodayake a gasar cin kofin duniya dan wasan bai samu zira koda kwallon daya ba raga. 

Andres Iniesta daLionel Messi da Xavi Hernandez, masu neman kyautar Ballon d'Or 2010.
Andres Iniesta daLionel Messi da Xavi Hernandez, masu neman kyautar Ballon d'Or 2010. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.