Isa ga babban shafi
CHAN

Nijar ta samu galabar Ghana a gasar CHAN

A gasar cin kofin kwallon kasashen Afrika Ta CHAN dake gudana a kasar Sudan kasar Jamhuriyar Nijer ta kafa tarihi inda ta samu nasarar tsallakewa zuwa buga wasannin Quarter Final a karon farko bayan ta doke Ghana da ci daya mai ban haushi.Kasar Jamhuriyyar Nijer dai bata taba shiga gasar kwallon kafa ba ta kasashen Africa sai a wannan karon amma kuma sun nuna bajintarsu inda suka kora kasar Ghana gida wacce ta taba lashe kyautar Azurfa a gasar da aka taba gudanarwa a shekarar 2009.A yanzu haka dai ‘yan wasan Nijar zasu kara ne da ‘yan wasan kasar Sudan a wasa ta gaba da za’a gudanar a ranar Juma'a  

Tambarin gasar CHAN da ake gudanarwa a kasar Sudan a bana.
Tambarin gasar CHAN da ake gudanarwa a kasar Sudan a bana.
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.