Isa ga babban shafi
wasanni

Badminton :Wassa ta kasa da kasa

A kwamballar wassar Badminton, ta All England Open a kasar Britaniya ,Lee Chong Wei, dan kasar Malasiya ,wanda kuma a yanzu haka shi ne ke rike da kofin wassar , ya fusata ,bayan da alkalin wassar ya mushi kashedi a lokacin da ya ke karawa da Bao Chunlai dan kasar Cana.Ya kuma ki ya ce wani abu ga yan jarida kan lamarin.Hukumar kwallon kafa ta kasar Cote-D’Ivoire, ta sanar da cewa, babu maganar dage Wassar tankade -da -raiyaye ,ta zuwa cin koffin Afrika na shekara ta 2012,da ya kamata kasar Cote-D’Ivoire da ta jumhuriyar Benin su kara a ranar 26 ga wanan wata na Maris.Wassar za ta gudana a Hilin kwalon na Houphouet Boigny da ke garin Abidjan .Za a kuma dokar matakan tsaron da su ka dace.A ranar 27 yan wassar ta Cote-D’Ivoire za su karawa da yan kasar Laberiya a game da zuwa wassanin Olympique na shekara ta 2012 a garin London na kasar Britaniya.   A kasar Sabuwaar Zelande ,wato New Zelande ko kuma Nouvelle Zelande,inda ake shirin gudanar da wassar cin koffin zari-ruga ta duniya nan da watani 6 masu zuwa,Ministan shirya wassani na kasar ,Murray Mc Cully,ba da dadaiwa ba , zai sanar ko dai birnin Christchurch ya tsaro ta fanin shiriya dokar nauyin wassar ko kuma a-a.Hukumar kwallon kaffa ta kasa da kasa,FIFA za ta soma dokar matakin ladabtarwa kan wasu al’kalai guda 6 da su ka yi alkalancin wassa tsakanin Boliviya da Lettoniya da kuma tsakanin Estoniya da Bulgariya da ake gani a koye magudi da tsantsar coge a ciki. 

Yar kallon wassar Badminton
Yar kallon wassar Badminton Reuters/Sean Gardner
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.