Isa ga babban shafi
Wasanni

Wassanni : Cricket da kwallon kafa

Hukumar kulla da wassar Cricket ta kasa da kasa ,ta taimakama hukumar wassar Cricket ta Sabuwar kasar Zelande, da kudi dallar Amurika milyon daya domin sake gina cibiyar hukumar da zilgizar kasa ta ruguza a cikin watan Febriyeru.Hukumar kwallon kaffa ta kasar Ingla, ta sa hannu kan wata rijejeniya da tashar talbajin ta Sky da ta shahara wajen labarin wassani,na kudi Pan milyon 195,wato milyon 220 naYiro wanan kuma na tsawon shekaru 3.  Denis Oswald, shugaban kungiyar Olympique,ya sanar da cewa duk shekara ta allah ,hukumar na kashe kudi milyon 50 na Dallar Amurika kimaninYiro milyon 35 kan binciken ‘yan wassa masu anfani da kwayoyi masu kara kuzari,a wassanin bazara kawai. A game da rubuta sunayen kwararin ‘yan wasa a kan litafin Alforma na zauren karamawa na duniya , na kasar Amurika ,a cikin watan Ugusta mai zuwa sunan Dennis Rodman dan kasar Amurika ,da kuma na Arvydas Sabonis dan kasar Lituani ,duk kasu tsofafin yan wassar kwando na kungiyar NBC, zai samu shiga.Mai take baya ga yan wassar kwallon kafa ta AS- Roma a Italia,dan kasar France,Phillippe Mexes ,an mushi aiki ga gwywar kafar hagu,bayan jimuwar da ya samu a lokacin wasar da su ka yi da kungiyar Juventus a ranar lahadin da ta gabata.A game da wassar kassancewa a cikin waanda za su karawa wajen cin koffin kungiyar kasashen turai a shekara ta 2012,a ranar 3 ga watan Yuni kasar France da ta Belarus za su karawa,kafin su kara da Albaniya a ranar 2 ga watan Satumba da kuma Roumaniya a ranar 6 ga watan na Satumba . 

Yan wassar Cricket na kasar India
Yan wassar Cricket na kasar India REUTERS/Vivek Prakash
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.