Isa ga babban shafi
wasanni

Laurent Blanc zai yi magana

Binciken ma’aikatar wassani da motsa jiki ta France ,wanda ministar Chantal Jouanno ta jagorenta da kanta ,da kuma bincike na 2 da hukumar kwallon kaffar kasar ta gudanar,duk sun share zargin da ake ma Laurent Blanc mai horar da ‘yan wasar kasar a game da dagigiyarnan kan maganar kabilanci da ta kunno kai a cikin zancen kwallon kaffa.To sai dai har yanzu da sauren runa a kaba,domin sai ranar Alhamise ne mambobin hukumar za su yanke hukumci kan maganar baki daya. Laurent Blanc zai yi furuci kan maganar a ranar Juma’a ta kafar talbajin mai zaman kanta a cikin labaranwassani na karfe 8 na yamma.Shugaban hukumar kwallon kaffa ta duniya Sepp Blatter ya maganta kan wani sabon korafi na cewa lamarin cin hanci da karbar rashawa sun mamaye hukumar ta FIFA.Sepp Blatter ya ce mutane sun bambanta ,ba zai iya dokar fansar kowa ba amma a game da hukumar ya na yi bakinrai bakin fama domin hukumar ta kassance bata da wani tambo kan lamari karbar cinhanci da rashawa.Lassana Diarra mai buga wassa a tsakiyar hilin kungiyar Real Madrid ta kasar Espagne na neman canji zuwa wata kungiya domin ya samu taba leda wajen cin koffin turai ta 2012.Lassana Diarra ya furuta haka ne acin jaridar Marca mai sa ido kan wassani da maganar yan wassa.Shugaban hukumar tseran motoci ta kasa da kasa ,Max Mosley da ya shigar da kare kan kasar Ingla na cewa ba ta kare incin shi ba,to a yau kotun kare hakin dan adam ta kasashen turai ta yi watsi da karen. 

Mai horar da yan kwallon France Laurent Blanc
Mai horar da yan kwallon France Laurent Blanc Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.