Isa ga babban shafi
UEFA

Za a hanzarta samar da visa ga masu zuwa gasar nahiyar Turai

Hukumomin Kasar Poland tace za ta za ta sanya wani tsarin da zai sa a rinka samar da takardun visa cikin sauki da kuma sauri, saboda ganin an an sami nasara zirga zirgar jama’a a yayin wasanin cin kofin kasashen turai da take shirin daukar nauyi shi tare da makwabciyarta Ukrain a shekara mai zuwa.Mataimakin ministan harkokin waje na kasar ta Polanda Jan Borkowski, ya ce Za a sami dandazon ‘yan wasa, ‘yan kallo, jami’an UEFA da na FIFA, likitoci da SS zuwa kasashen, don kasha kwarkwatar ido.Ministan ya ce duk wanda ya sami tikitin wasannin, to yana da damar samun visa.Za dai a yi wasannin na UEFA tun daga ranar 8 ga watan Yuni zuwa daya ga wata Yulin shekarar 2012. 

UEFA
UEFA EURO 2008
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.