Isa ga babban shafi
Wasanni

Tennis da Cricket

A kwamballar tennis ta Wimbledon ,yau dai kwanaki na 3 da somawa,sai dai kuma ruwan sama kamar da bakin kwarya sun hana a gudanar da wassar .Yan kallo sun yi jiran sa o i sama da 3,malka ta hana kowa ya ga warai a hilin wassar.An dage wassar da ya kamata ta gudana tsakanin Venus Williams yar kasar Amurika da ta kassance lamba wane so 5 a wassar ,da kuma yar kasar Japon Kimiko Date-Krumm sai karfe 12 agongon TU.Dan kasar Jamaika, Usain Bolt da ya kassance mai rike da kambun gudun mita 100 da dari 2 na duniya , ba zai hallarci gassar gudun kasar Jamaika ba da za ta fara a satin gobe cewar hukumar gudun kafa ta kasar.Sabili da bai rubuta sunanshi ba a cikin jeran sunayen masu hallarta .   Kungiyar yan tseran basukur ta RadioShack ta sanar da cewa ta na da yan tsere guda 9 da za su hallartar tseran basukur na tour de France, sai dai babu Lance Amstrong daga ciki sabili da ya yi murabuse daga lamuren sukuwar basukur,kuma a yanzu haka hukumar binciken kasar Amurika kan anfanin da kwayoyi masu kara kuzari ta na biye da shi kan bincike.A gobe ne ranar Olympique ta kasa da kasa,hukumomin Olympique sun ci gaba da yin anfani da kafofin sadarwa na zaman domin kassance tare da matassa cikin muamulla.Bayan talbajin Kafofin sun hada da Youtube, Twitter ,Facebbok.Har yanzu dai babu labarin ko jami’an hukumar wassar cricket ta kasar Srilanka da ya kamata su je India a yau ,ko sun je koko ba su je ba,domin tautaunawa kan maganar harancin da ake sun azama wasu yan wassar kasar ta Srilanka kussan 12. 

Hilin wassar a kasar Gabon
Hilin wassar a kasar Gabon Wikipédia/(CC)/Starms
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.