Isa ga babban shafi
FARANSA

Za’a biya Raymond Domenech kudi bayan korarsa

Shugaban hukumar kwallon kafar kasar Faransa Noel Le Graet yace Tsohon mai horar da ‘yan wasan kasar Faransa Raymond Domenech zai karbi kudi sama da Euro miliyan 900 bayan amincewa da bukatar biyansa kudi bayan korarsa daga aikin horar da ‘yan wasa.An dai kori Mr Domenech bisa rikicin da ya biyo baya tsakanin shi da ‘yan wasansa da kuma rashin tabuka wani abin azo gani da ‘yan wasan suka yi a gasar cin kofin duniya da aka gudanar a kasar Africa ta kudu a shekarar bara. 

Tsohon mai horar da 'yan wasan Faransa Raymond Domenech.
Tsohon mai horar da 'yan wasan Faransa Raymond Domenech. REUTERS/Charles Platiau
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.