Isa ga babban shafi
kasuwar 'Yan wasa

An rufe kasuwar cinikin ‘yan wasa a Turai

Wani sakamakon bincike da aka fitar na nuna cewa manyan kungiyoyin kwallon kafa a Ingila da Spain da Itali sun kashe kudi kusan Dala Biliyan $2b wajen sayen sabbin ‘yan wasa a bana. Bayan rufe kasuwar a daren jiya laraba.Binciken wanda kamfanin Deloitte ya gudanar an bayyana cewa Ingila ce kan gaba inda kugiyoyin kwallon kafar kasar suka kashe kusan kudi Dala Miliyan 800.Kungiyoyin kwallon kafa kuma a Itali suka kashe kudi Dala Miliyan 651, a kasar Spain kuma Dala Miliyan 488.A Ingila dai Manchester United da Manchester City da Chelsea da Liverpool da Arsenal su ne manyan kungiyoyin kwallon kafa da suka ci kasuwar cinikin ‘yan wasan inda kowannensu ya kashe kudi sama da dala Miliyan 81, wato kashi 66 cikin dari na kudaden da aka kashe a kasuwar ‘yan wasan.  

Cesc Fabregas Dan wasan Arsenal bayan ya koma Barcelona
Cesc Fabregas Dan wasan Arsenal bayan ya koma Barcelona REUTERS/Gustau Nacarino
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.