Isa ga babban shafi
Marathon

Tsoho mai shekaru 100 a tseren gudun gasar Marathon

Fauja Singh shi ne tsoho mai shekaru 100 da ya yi gudun kusan sa’o’I 9 a gasar Marathone da aka kammala a Canada.Mista Singh dan asalin kasar Indiya ne, daga baya ne ya koma da zama a London.Kuma Mista Singh ya kasance mutum mai yawan shekaru da ya shiga gasar duk da cewa shi yazo na 3,850. Amma ya doke wasu mutane biyar a bayansa.A hira da manema labarai, Mista Singh yace ya fara sha’war gudu ne shekaru 11 da suka gabata bayan mutuwar iyalinsa matarsa da dansa. Kuma Yace a kowace rana yana gudun mile 10 a kowace safiya. 

Fauja Singh tsoho mai shekara 100 a gasar Marathon
Fauja Singh tsoho mai shekara 100 a gasar Marathon @Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.