Isa ga babban shafi
La Liga

Ronaldo yana hararen kwallaye 100 a Madrid

A karshen makon nan Cristiano Ronaldo ya zira kwallaye uku a raga bayan Real Madrid ta lallasa Malaga ci 4-0, kuma yanzu nan da dan lokaci kadan ne zai yi bukin zira kwallaye 100 a Real Madrid bayan zira kwallaye 98.A ranar Laraba Real Madrid zata kara da Villareal, kuma Ronaldo yace yana fatar ganin sun samu nasarar lashe wasan tare da kafa tarihin zira kwallaye 100.Yanzu haka a La Liga Lavente ce ke jagoranci Table a karon farko tun bayan shekaru 102 a tarihin gasar.Lavente wacce ta tsallake rijiya da baya a kakar wasn bara, tana jagorantar Table ne da maki 20, maki daya tsakaninta da Real Madrid maki biyu kuma tsakaninta da Barcelona.Barcelona da ke jagorantar Table a makon jiya ta yi kunnen doki babu ci tsakaninta da Sevilla bayan Lionel Messi ya barar da Panalty bugun da kai sai gola a filin wasa na Camp Nou. 

Cristiano Ronaldo dan wasan Real Madrid.
Cristiano Ronaldo dan wasan Real Madrid. Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.