Hungary
Dan kasar Hungary Tsohon dan wasan Turai Albert ya mutu
Florian Albert, tsohon dan wasan Hungary kuma tsohon gwarzon dan wasan turai ya mutu a asibiti yana da shekaru 70 sanadiyar fama da ciwon zuciya.Albart shi ne dan wasa tilo daga kasar Hungary da ya taba lashe kyautar gwarzon dan wasan Turai a shekarar 1967 bayan ya doke dan kasar Ingila dan wasan Manchester United Bobby Charlton wanda ya zo a matsayin na biyu.Daukacin rayuwarsa Florian Albert ya taka leda ne a club din Ferencvaros da ke kasarsa Hungary inda ya zira kwallaye 351 a raga.
Wallafawa ranar: