Tennis
Nadal ya fice gasar Paris Masters
Fitaccen dan wasan Tennis Rafeal Nadal ya fice daga gasar Paris Masters da za’a fara gudanarwa a makon gobe.A cewar Nadal a shafinsa na Facebook ya fice ne domin shiryawa gasar Tennis WTA ta duniya da za’a gudanar a birnin London a badi.Nadal na daya daga cikin fitattun ‘yan wasan Tennis da suka tsallake zuwa gasar da suka hada da Novak Djokovic, Andy Murray, Roger Federer and David Ferrer
Wallafawa ranar: