Isa ga babban shafi
FIFA

Kafafen yada labaran Birtaniya sun yi kiran Blatter ya yi murabus

Kafafen yada labaran kasar Birtaniya sun bukaci Sepp Blatter shugaban hukumar FIFA ya yi murabus daga mukaminsa bisa kalamansa na rashin mutunta matsalar wariyar launi fata a kwallon kafa.Blatter ya fara fuskantar kalubalen ne bayan kalamansa kan batun nuna wariyar launin fata a filin wasan kwallon kafa, inda yace ‘yan wasan da aka nunawa wariya zasu iya sasansawa da juna cikin filin wasa ta hanyar gaisawa da hannu.Blatter ya furta kalaman ne a wata hira da kafar Telebijin ta CNN akan kasar Ingila inda ake tuhumar manyan ‘yan wasa wajen zagi da nuna wariyar launi fata ga abokan hamayya a wasannin Premier League.Daga cikin takaddamar shi ne rikicin John Terry tsakanin shi da Anton Ferdinand kanin Rio Ferdinand.A shafinsa na Twitter Rio Ferdinand ya yi kakkausar Suka ga kalaman Blatter.Kalaman na Blatter na zuwa ne dai dai da lokacin da Hukumar FA ta Ingila ta tuhumi Luiz Suarez kan nuna wariya ga Patrice Evra dan kasar Faransa mai taka leda a Manchester United.A wata hira da kafar Telebijin din kasar Faransa Evra yace Suarez ya zage shi kusan sau goma a lokacin wasa tsakanin Manchseter United da Liverpool da aka ta shi kunnen doki. 

Joseph Blatter shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA.
Joseph Blatter shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA. REUTERS/Arnd Wiegmann
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.