Isa ga babban shafi
Cricket

Babban Jami'in Hukumar Cricket zai kawo karshen wa’adinsa a badi

Hukumar wasan Cricket ta ICC ta sanar a shafinta na Internet cewa a watan Junin badi ne babban Jami'in zartarwar hukumar, Haroon Lorgat zai kawo karshen wa’adin shugabancinsa.Mista Lorgat shi ne ya jagoranci mayar da ginin Hedikwatar hukumar wasannin a Dubai tare da jagorantar kawo karshen takaddamar da aka kwashe watanni ana yi kan rikicin ‘yan wasan kasar Pakistan da aka yanke wa hukuncin dauri a gidan yari bayan kama su da laifin yin coge a wasan.Shugaban wasannin na duniya Sharad Pawar ya jinjinawa Haroon dangane da rawar irin rawar day a taka ga ci gaban wasannin Cricket. 

Haroon Lorgat Shugaban zartarwar hukumar Cricket ta ICC
Haroon Lorgat Shugaban zartarwar hukumar Cricket ta ICC REUTERS/Bobby Yip
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.