Isa ga babban shafi
Ingila

Chelsea 2 - 1 Man City

A wasan Premier ta ingila da aka gudanar a daren jiya Chelsea ta doke Manchester city ci 2-1, bugun daga kai sai mai tsaron gida ne da Frank lampard ya buga ya ba Chelsea wannan nasarar.

Mai tsaron gidan Manchester City, Joe Hart
Mai tsaron gidan Manchester City, Joe Hart Reuters
Talla

Mario Balotelli ne ya fara zirawa City kwallonta a ragar Chelsea, kafin zuwa rabin lokaci ne kuma Raul Meireles ya barkewa Chelsea kwallonta.

Sai dai a farkon dawowa rabin lokaci ne ‘yan wasan Manchester city suka dawo su 10 bayan da alkalin wasa ya daga jan kati ga Clichy wanda hakan ne kuma ya budewa Chelsea hanyar lashe wasanta.

Tun fara kakar wasan bana sai yanzu ne aka samu galabar Manchester city a Premier. Sai dai, City ce ke ci gaba da jagorancin Table amma maki biyu tsakaninta da Manchester United, Cheslea ce kuma a matsayi na uku, maki 7 tsakaninta da City.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.