Isa ga babban shafi
CAF

CAF ta fitar da jerin wadanda zata zaba Jarumanta a Afrika

Hukumar dake kula da kwallon kafa a Africa ta CAF ta fitar da jerin ‘yan wasan da zata zaba gwarzon Africa a bana hadi da gwarzon koci da kungiyoyin maza da mata a Africa. 'Yan Jaridu ne da Jagoran kungiyoyin kwallon kafa da masu horar da 'Yan wasa zasu zabi wadanda zasu lashe kyautar a ranar 22 ga watan Disemba a birnin Accra kasar Ghana.

Tambarin Hukumar kwallon kafa tare da Tambarin Glo kamfanin Sadarwa da zai dauki nauyin bukin bada kyautar
Tambarin Hukumar kwallon kafa tare da Tambarin Glo kamfanin Sadarwa da zai dauki nauyin bukin bada kyautar CAF
Talla

A jerin sunayen Zakaran dan wasa, CAF ta ware:
(a) Andre Ayew (Olympique Marseille dan kasar Ghana)
(b) Samuel Eto’o (Anzhi Makhachkala dan kasar Kamaru)
(c) Seydou Keita (Barcelona dan kasar Mali)
(d) Moussa Sow (Lille dan kasar Senegal)
(e) Yaya Toure (Manchester City dan kasar Cote d’Ivoire)

A bangaren ‘Yan wasan da ke taka kwallo a gida, CAf zata zabi gwarzonta ne tsakanin:
(a) Oussama Darragi (Esperance Tunis dan kasar Tunisia)
(b) Zouhir Dhaouadi (Club Africain dan kasar Tunisia)
(c) Banana Yaya (Esperance dan kasar Kamaru)

kasashen da CAF kuma zata zabi fitacciya a bana sun kunsh:

(a) Botswana
(b) Cote d’Ivoire
(c) Nijar
(d) Tunisia

A bankaren mata CAF ta ware:
(a) Kamaru
(b) Najeriya
(c) Africa ta Kudu

A bangaren mai horar da ‘yan wasa akwai:
(a) Harouna Doula (Nijar)
(b) Nabil Maaloul ( Kocin Esperance ta Tunisia)
(c) Stanley Tshosane (Botswana)

cikin wadand`a CAF zata karrama matsayin fitattun ‘yan wasa akwai:

Mustapha Hadji (Morocco)
Austin ‘Jay-Jay’ Okocha (Najeriya)

Jaruma a bangaren Mata CAF ta ware:
(a) Nompumelelo Nyandani (Africa ta Kudu)
(b) Perpetua Nkwocha (Najeriya)
(c) Miriam Paixao Silva (Equatorial Guinea)

Cikin Alkalan wasa CAF ta ware:
(a) Alioum Neant (Kamaru)
(b) Noumandiez Doue (Cote d’Ivoire)
(c) Djamel Haimoudi (Algeria)
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.