Equatorial Guinea ta raba gari da kocinta
Kocin kasar Equatorial Guinea Henri Michel, dan kasar Faransa ya ajiye aikin shi, wata daya a fara gudanar da gasar cin kofin Afrika inda kasar ke daya daga cikin masu daukar nauyin gudanar da gasar.
Wallafawa ranar:
Mista Michel wanda tsohon jagoran ‘yan wasan Faransa ne kuma tsohon koci ya ajiye aikinsa ne bayan da wani babban jami’in hukumar wasanin kasar ya nemi ya yi masa katsalandan ga aikinsa na shirye shiryen gudanar da gasar Cin kofin Nahiyar Afrika da za’a fara a ranar 21 ga watan Janairu.
Yanzu haka kuma hukumar wasannin ta maye gurbin Michel da Casto Nopo a matsayin sabon koci.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu