Premier
Henry ya dawo kuma ya fitar da Arsenal Kunya
Thierry Henry ya dawo kuma ya fitar da Arsenal kunya a gasar FA da aka gudanar a daren jiya, inda ya kafa tarihin zira kwallo a ragar Leeds United a kwallonsa ta farko bayan dawowarsa Emirates. Mintina 11 da saka dan wasan ne ya zira kwallo a raga, kwallonsa ta 227 ga Gunners.
Wallafawa ranar:
Talla
Henry mai shekaru 34 na haihuwa ya bar Arsenal ne a shekarar 2007 kuma shi ne dan wasan da yafi zira kwallaye a raga, a makon jiya ne Arsenal ta karbi Aron Henry na tsawon watanni biyu daga kungiyarsa ta New York Red Bulls.
Arsene Wenger dai yace wannan mafarki ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu