Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Barcelona ta doke Madrid a Copa Del Ray

Mourinho ya sake shan kashi a bana hannun Bercelona a filin wasa na Santiago Bernabeu, duk da Real Madrid ce ta fara zira kwallo amma daga bisa ni Barcelona ta zirara kwallaye biyu inda aka tashi wasan ci 2-1.

Eric Abidal yana murnar kwallon da ya zira a ragar Madrid tare da Carlos Puyol wanda ya zira kwallon farko a Copa Del Ray a filin wasa na Santiago Bernabeu
Eric Abidal yana murnar kwallon da ya zira a ragar Madrid tare da Carlos Puyol wanda ya zira kwallon farko a Copa Del Ray a filin wasa na Santiago Bernabeu REUTERS/Susana Vera
Talla

Bayan dawowa rabin lokaci ne ‘yan wasan bayan Barcelona Carles Puyol da Eric Abidal suka zira kwallaye a ragar Madrid bayan kwallon da Ronaldo ya fara zirawa a ragar Barcelona.

Wannan ne karo na uku Barcelona ke samun galanar Madrid cikin shekara a filin wasa na Santiago Bernabeu, har yanzu kuma Pep Guardiola kocin Barcelona, Madrid bata samu galabar shi ba a Bernabeu tun fara aikin shi a kakar wasanni hudu.

Wannan dai wasan Quarter Final ne kuma akwai karawa ta biyu tsakanin abokan hamayyar a filin wasa na Nou Camp gidan Barcelona.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.