Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

United ta doke Arsenal, Mourinho ya yi cacar baki da ‘yan wasan shi

A Premier League a Ingila, Manchester city da Manchester United dukkaninsu sun samu nasarar lashe wasanninsu a karshen mako, a Spain kuma Real Madrid ke ci gaba da jagorancin Table sai dai wata cacar baki ta kaure tsakanin ‘Yan wasan Madrid da Mourinho.

Jose Mourinho a lokacin da Madrid ta sha kashi hannun Barcelona a gasar Copa Del Ray
Jose Mourinho a lokacin da Madrid ta sha kashi hannun Barcelona a gasar Copa Del Ray REUTERS/Felix Ordonez
Talla

Ingila

A ingila Mario Balotelli ne ya zira kwallon karshe a bugun daga kai sai mai tsaron gida, wanda ya bai wa Manchester city damar nasarar doke Tottenham ci 3-2.

Da farko dai City ce ta fara zira kwallo biyu a raga kafin Tottenham ta barke kwallayen inda aka dawo ci 2-2. A mintinan karshe ne Mario Balotelli ya jefa kwallo ta uku a ragar Tottenham.

Yanzu haka kuma maki uku ne ke tsakanin City da Manchester United, bayan tasha da kyar hannun Arsenal ci 2-1.

Liverpool kuma tasha kashi ne hannun Bolton ci 3-1,

Wasa tsakanin Chelsea da Norwich an tashi ne babu ci.

SPAIN

A la liga kuma Real Madrid ta doke Athletic Bilbao ci 4-1, Cristiano Ronaldo ne ya zira kwallaye biyu a raga a bugun daga kai sai mai tsaron gida.

Messi kuma ya zira kwallaye uku ne bayan Barcelona ta lallasa Malaga ci 4-1.

Mujallar wasanni ta Marca a kasar Spain ta ruwaito wata cacar baki da aka samu tsakanin Mourinho da ‘yan wasan shi. Bayan sun sha kashi hannun Barcelona a tsakiyar makon jiya.

Duk da Real ta lashe wasanta a karshen mako amma Mourinho ya sha shewa ga magoya bayan Madrid a Bernabeu.

Sai dai Mourinho yace wannan ba damuwar shi ba ne domin haka kwallo ta gada adaga masoya Madrid a Bernabeu, domin hakan ta faru ga fitattatun ‘Yan wasa irin su Zidane, Ronaldo da Cristiano (Ronaldo), wadanda suka yi suna a Bernabeu.

jaridar dai ta Ruwaito Muourinho yana cacar baki tsakaninshi da Sergio Ramos, inda mourinho ya zarge shi wajen rashin make Carles Puyol a lokacin da zai zira kwallo a raga, amma kuma Sergio Ramos ya mayar da martanin cewa ba laifin shi ba ne laifin Pepe ne.

Italiya

A Seria A, AC Milan ta doke Novara ci 3-0, Zlatan Ibrahimovic da Robinho ne suka zirawa AC Milan kwallayenta a raga. Kuma maki daya ne yanzu tsakaninta da Juventus, amma Juve ta doke Atlanta ci 2-0.

Jamus
A Bundesliga Borussia Dortmund da ke rike da kofin ta samu nasarar lallasa Hamburg ci 5-1, wanda ya bata damar bin sahunsu Bayern Munich Schalke 04 a saman Table.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.