Isa ga babban shafi
Tennis

Clijsters ta doke Wozniacki a Autralian Open

Kim Clijsters ta doke fitacciyar ‘yar wasan Tennis ta duniya Caroline Wozniacki a gasar Autralian Open. Clijsters ‘Yar kasar Belguim mai shekaru 28, tun da farko tace bayan kammala gasar Australian Open ne zata yi bankwana da Tennis, yanzu haka kuma zata kara ne da Victoria Azarenka a wasan kusa dana karshe.

Kim Clijsters 'Yar kasar Belgium a gefen Hagu tana gaisawa da h Caroline Wozniacki ta Denmark bayan kammala wasansu ta Quarter Final
Kim Clijsters 'Yar kasar Belgium a gefen Hagu tana gaisawa da h Caroline Wozniacki ta Denmark bayan kammala wasansu ta Quarter Final REUTERS/Daniel Munoz
Talla

Da farko dai Victoria Azarenka ta Belarus ta doke Radwanska ne ‘yar kasar Poland a wasan Quarter Final.

A akwai wasannin Quarter final da za’a ci gaba da gudanarwa a yau tsakanin:

Ekaterina Makarova (Rasha) da Maria Sharapova (Rasha)

Sara Errani (Italiya) da Petra Kvitova (Czeck)

A bangaren maza kuma akwai wasa tsakanin:

Novak Djokovic (Serbia) da David Ferrer (Spain)

Andy Murray (Birtaniya) da Kei Nishikori (Japan)

Juan Martin del Potro (Argentina) da Roger Federer

Tomas Berdych (Czeck) da Rafael Nadal (Spain)

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.