Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Ribery ya dawo a Munich, Gerrard ya bukaci masoya Liverpool nuna da’a

A Bundesliga a kasar Jamus, Bayarn munich zata yi lale marhabin da dawowar Franck Ribery a wasan da zasu kara a ranar Assabar da Wolfsburg, bayan kwashe kawanki yana jinya. A Ingila, Jagoran ‘yan wasan Liverpool Steven Gerrard ya bukaci magoya bayan kungiyar nuna dattaku da da’a a wasan gobe da zasu karbi bakuncin Manchester United a filin wasa na Anfield a gasar FA.

Dan kasar Faransa Franck Ribery  Dan wasan Bayern Munich,
Dan kasar Faransa Franck Ribery Dan wasan Bayern Munich, Reuters / Michael Dalder
Talla

A jiya Frank Ribery yana cikin tawagar Bayrn Munch da suka gudunar da horo a sansaninsu.

Wasan gobe ita ce zata kasance wasan Farko ga Ribery tun bayan ba shi jan kati da alkalin wasa ya yi a wasansu da Cologne kafin hutun Kirsemeti.

Ingila

Jagoran ‘yan wasan Liverpool Steven Gerrard ya bukaci magoya bayan kungiyar nuna dattaku da da’a a wasan gobe da zasu karbi bakuncin Manchester United a filin wasa na Anfield a gasar FA.

Wannan ne karo na farko da Liverpool zata sake karawa da United tun lokacin da aka haramtawa dan wasanta Luis Suarez buga wasanni 8 bayan nuna wariyar launin fata ga dan wasan Manchester, Patrice Evra.

Spain

Real Madrid zata dawo ne La liga domin ci gaba da jagorancin Table, inda zata karbi bakuncin Real Zaragoza a gobe Assabar bayan tasha kashi hannun Barcelona a tsakaiyar mako a gasar Copa del Ray.

Maki biyar ne tsakanin Barcelona da Madrid a saman Table, kuma Madrid tana matsin lamba ne ga Barcelona wacce zata bakunci kungiyar Villarreal bayan Madrid ta buga wasanta.

Sai dai yanzu haka Barcelona ta hadu da cikas bayan kammala Clasico domin ‘yan wasanta biyu Andreas Ineista da Alexis Sanchez sun samu rauni, Iniesta zai kwashe tsawon makwanni uku yana jinya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.