Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Keshi zai yi amfani da matasa a wasan Najeriya da Liberia

A yau ne Najeriya zata buga wasan sada zumunci da kasar Liberia a birnin Manrovia, Stephen Keshi ya bayyana ‘Yan wasa Ashirin da zasu bugawa Najeriya wasan kuma dukkanin ‘yan wasa ne masu taka leda a gida.

Stephen Keshi, Kocin Super Eagles na Najeriya
Stephen Keshi, Kocin Super Eagles na Najeriya Next
Talla

Akwai dai ‘yan wasan kungiyar Kano Pillers guda biyu wato Papa Idris da Reuben Gabriel, Sai dai ‘yan wasan Heartland ne suka fi yawa cikin kungiyoyin kwallon kafar kasar, inda aka zabi ‘yan wasa hudu wato Obinna Nwachukwu da Kabiru Umar da Kingsley Salami da Ibenegbu, Eyimba kuma an zabi ‘Yan wasanta uku ne.

Wannan wasan shiri ne da Najeriya ke yi domin wasan da Super Eagle zasu buga da Rwanda a ranar 29 ga watan Fabrairu don neman shiga gasar cin kofin Afrika a shekarar 2013.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.