Isa ga babban shafi
Boxing

Vitali Klitschko yace mulkin danniya ake yi a Ukraine

Fitaccen dan damben Boxing na kasar Ukrain, Vitali Klitschko ya yi gargadin cewa zanga-zangar da ke ci gaba da kadawa a Syria zata iya fara kadawa a kasar shi, inda ya danganta ana gudanar da mulkin kama karya a Ukraine.

Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing  tare da dan uwansa Wladimir a fagen dambe kafin karawarsa da ya lashe kyautar ajin masu nauyi a karawarsa da dan kasar Poland Tomasz Adamek
Vitali Klitschko Zakaran Damben Boxing tare da dan uwansa Wladimir a fagen dambe kafin karawarsa da ya lashe kyautar ajin masu nauyi a karawarsa da dan kasar Poland Tomasz Adamek REUTERS/Peter Andrews
Talla

A wata hira da wata kafar yada labarai a Ukraine, Vitali Klitschko yace mulkin danniya ake gudanarwa a kasar Ukraine kuma kalaman shi na zuwa kwanaki hudu da kare kambunsa na zakaran Damben Boxing ajin masu nauyi.

Vitali Klitschko yana neman a zabe shi ne Dan Majalisaer kasar kuma ya dade yana neman tabbatar da ‘Yancin Demokaradiya daga shugaban kasar ukraine Viktor Yanukovich.

A shekarar 2004 da aka gudanar da wani juyin jiuya hali a kasar, Vitali Klitschko ya goyi bayan tsohon shugaban kasa Viktor Yushchenko domin kalubalantar Yanukovych.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.