Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

United ta dare Tebur na Premier, Messi ya zira kwallaye 50 a bana

A Ingila Manchester United ta dare saman Tabur na Premier bayan doke West Bromwich Albion ci 2-0, kuma Wayne Rooney ne ya zira kwallayen a raga, Manchester city kuma ta sha kashi hannu Swansea city ci 1-0.

Dan kasar Argentina Lionel Messi dan wasan kungiyar Barcelona lokacin da yake murnan zira kwallo a raga
Dan kasar Argentina Lionel Messi dan wasan kungiyar Barcelona lokacin da yake murnan zira kwallo a raga REUTERS/Albert Gea
Talla

Sai dai Roberto Mancini yace kofin Premier na Manchester City ne duk da kashin da ya sha hannun Swansea bayan kwashe watanni yana jagorancin Tebur. Yanzu dai maki daya ne United taba Manchester City a Tebur.

SPAIN

A jiya Lahadi ne Lionel Messi ya yi bukin zira kwallaye 50 a raga a bana bayan Barcelona ta doke Racing Santande ci 2-0. Sai dai har yanzu tazarar maki 10 ne tsakanin Barcelona da Real Madrid.

A gasar zakarun Turai dai Messi ya zira kwallaye 5 a ragar Bayarn Leverkusen.

Kuma yanzu akwai tazarar kwallaye 10 tsakanin Messi da Cristiano Ronaldo, kodayake Ronaldo shi ne ke da yawan kwallaye 32 a La liga.

Madrid dai ta sha da kyar ne hannun Real Betis ci 3-2, kuma Madrid na neman lashe kofin La liga ne karon farko tun a shekarar 2008.

ITALIYA

A Seria A, ta Italiya, AC Milan ta sake samun yawan maki a jagorancin Tabur inda ta doke Lecce ci 2-0, bayan kuma wasa tsakanin Juventus da Genoa an tashi babu ci.
Antonio Nocerino ne da Zlaten Ibrahimovic suka zirawa Milan kwallayen ta a raga.

Cagliari kuma ta sallami kocinta, Davide Ballardini watanni hudu da kama aikin shi, kuma shi ne koci na 15 da aka sallama a bana a Seria A tsakanin kungiyoyin Italiya.

JAMUS

A Bundesliga ta kasar Jamus, Mario Gomez ya zira kwallaye 3 a raga bayan da Bayern Munich ta lallasa Hoffenheim ci 7-1. Kuma yanzu maki 5 ne tsakanin Bayarn da Borussia Dortmund mai rike da kofin Bundesliga a bara.

FARANSA

A Faransa kuma Paris Saint-Germain ta sha da kyar hannun Dijon, inda a mintinan karshe Kevin Gameiro ya samu nasarar zirawa PSG kwallo ta biyu bayan ana ci 1-1.

Yanzu haka dai maki daya ne Carlo Ancelotti ya ba Montpellier wacce ta doke Caen ci 3-0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.