Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

United zata karbe Tebur hannun City idan ta doke Fulham

A Premier League ta Ingila Manchester City ga alamu ba zata iya jagorancin Tabur ba domin a karshen mako ta yi kunnen doki ci 1-1 da Stoke City, kuma a yau Litinin idan Manchester United ta doke Fulham zata dare Tebur da maki uku. A Faransa Montpellier ta dare saman Tebur da yawan kwallaye.

Dan wasan Stoke City, Peter Crouch a saman iska lokacin da zai harba kwallo a ragar Manchester City.
Dan wasan Stoke City, Peter Crouch a saman iska lokacin da zai harba kwallo a ragar Manchester City. REUTERS/Darren Staples
Talla

A Premier League yanzu maki daya ne tsakanin Manchester City da United, amma Manchester United zata iya karbe jagorancin Tabur idan har ta samu nasarar doke Fulham.

Bayan kammala wasan City da Stoke, Kocin City Roberto Mancini, ya ki hada hannu da kocin Stoke Tony Pulis tare da kauracewa manema labarai saboda rashin jin dadin sakamakon wasan.

Arsenal kuma da ke a matsayi na uku ta lallasa Aston Villa ne ci 3-0.
Bolton kuma ta samu nasarar wasan farko bayan matsalar Fabrice Muamba inda ta doke Blackburn ci 2-1.

Liverpool kuma tasha kashi ne hannun Wigan ci 2-1.

Wasa tsakanin Chelsea da Tottenham an tashi ne babu ci.

Faransa

A Faransa, Montpellier ta dare saman Tebur da yawan kwallaye bayan Paris Saint-Germain ta yi kunnen doki ci 1-1 da Bordeaux inda kuma Montpellier ta lallasa Saint-Etienne ci 1-0.

Montpellier dai ta farfado ne bayan ficewa gasar cin kofin Faransa.

Spain

A Spain, Cristiano Ronaldo ya kasance dan wasan da ya zira kwallaye 100 a raga cikin lokaci kankani a La liga, bayan ya zira kwallaye biyu a wasan da Real Madrid ta lallasa Real Sociedal ci 5-1.

Yanzu dai kwallayen Ronaldo 101 ne a wasanni 92 da ya ke bugawa Madrid.

Har yanzu dai maki shida ne tsakanin Barcelona da Real Madrid domin Barcelona ta doke Mallorca ci 2-0. Lionel Messi kuma yana cikin wadanda suka zirawa Barcelona kwallo a raga. Kuma yanzu Messi shi ne dan wasa na Farko a Turai wanda ya zira yawan kwallaye 55 a raga a kakar wasa inda ya share sunan Mario Jardel na Sporting Lisbon.

A La liga Kwallaye 35 ne Messi da Ronaldo suka zira a raga.

Italiya

A Seria A kuma Zlatan Ibrahimovic ya zira wa AC Milan kwallaye biyu wanda ya bata nasarar doke Roma ci 2-1.

Sai dai a Wasan Milan, ta yi hasarar dan wasanta Thiago Silva wanda ya ji rauni a kafar shi, kuma ana tunanin ba zai samu damar buga wasan Milan da Barcelona ba a wasan zakarun Turai da za’a gudanar a ranar Laraba a San Siro.

Juventus kuma da ke matsayi na biyu a Tebur ta doke Inter Milan ci 2-0.

Jamus

A Bundesliga kuma Borussia Dortmund da ke jagorancin Tabur ta doke Cologne ci 6-1. Nasarar da taba Dortmund kare makinta biyar da taba Bayern Munich, Duk da Bayern ta doke Hanover ci 2-1.

A ranar 12 ga watan Mayu ne Bayern da Dortmund zasu kece raini a wasan karshe ta cin kofin gasar Jamus a Berlin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.