Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Bayern ta lallasa Marseille, Milan ta haramtawa Barcelona zira kwallo a raga

A gasar Zakarun Turai zagayen Quarter Final, wasa tsakanin Barcelona da AC Milan an kwashe tsawon minti 90 ba tare da zira kwallo a raga ba saboda AC Milan ta kare gidanta. Amma Bayern Munich ta lallasa Marseille ci 2-0.

Franck Ribery Dan wasan Bayern Munich da dan wasan 'Olympique Marseille André Ayew a wasan zakarun Turai
Franck Ribery Dan wasan Bayern Munich da dan wasan 'Olympique Marseille André Ayew a wasan zakarun Turai Reuters
Talla

AC Milan dai ta yi kokarin kare gidanta ne, domin hana Barcelona zira kwallo a raga, kuma Milan sai ta sake yin haka a ranar Talata tare da zira kwallo a raga idan har zata samu hurumin karawa da Chelsea ko Benfica a zagayen kusa da karshe.

Bayern Munich yanzu ta sa kafar dama a zagayen kusa da karshe, inda akwai yiyuwar zata kara da Real Madrid wacce ta doke APOEL Nicosia ci 3-0 a karawar farko.

Mario Gomez ne da Arjen Robben suka zira wa Bayern kwallayenta a ragar Marseille.

A bana, Barcelona ce bata lashe wasanta ba cikin kungiyoyin da suka kai wa wata kungiya ziyara, Domin Real Madrdid da Chelsea da Bayern Munich dukkaninsu suna da kwarin giwarar tsallakwa zagayen kusa da Final.

A Tarihin gasar zakarun Turai wannan ne karo na farko da aka samu kungiyoyin da suka fara karbar bakuncin zagayen Quarter final basu samu nasarar lashe wasanninsu ba.

A wasan gaba da Barcelona da Milan zasu fafata, sai Barcelona ta yi da gaske domin idan Milan ta zira kwallo daya a raga, sai Barcelona ta zira kwallaye biyu a zama dai dai, idan kuma Milan ta zira kwallaye biyu a raga sai Barcelona ta zira kwallaye uku.

Kocin Barcelona Pep Guardiola yace ya zama Dole Barcelona ta zira akalla kwallaye biyu idan har zasu yi waje da AC Milan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.