Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Barcelona ta doke Getafe, Madrid zata kece raini da Atletico

Tazarar maki daya ne tsakanin Barcelona da Real Madrid, bayan Barcelona ta lallasa Getafe ci 4-0 kafin Madrid ta fafata da makwabciyarta Atletico Madrid a yau Laraba.

'Yan Wasan Barcelona, Pedro Rodriguez  Lionel Messi a lokacin da suke tabewa bayan Pedro ya zirara kwallo a ragar Getafe
'Yan Wasan Barcelona, Pedro Rodriguez Lionel Messi a lokacin da suke tabewa bayan Pedro ya zirara kwallo a ragar Getafe REUTERS/Albert Gea
Talla

Alexis da Messi da Pedro suka zirawa Barcelona kwallayenta a raga wanda ya bai wa Barcelona nasarar lashe wasanni goma ba tare da samun galabarta ba.

Guardiola, Kocin Barcelona yace sun sadaukar da wannan nasarar ga Eric Abidal wanda aka yi wa dashen Anta a jiya Talata.

A makwanni uku da suka gabata, Real Madrid taba Barcelona tazarar maki 10 amma yanzu Barcelona ta hura wuta inda ta lashe wasanninta goma, bayan Madrid ta yi kunnen doki da Osasuna da Villareal da Valencia.

A yau Laraba ne ‘yan wasan Mourinho zasu bakunci Atletico Madrid, amma sai Madrid ta yi da gaske domin kare makinta uku.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.