Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

Bayern Munich zata kece raini da Real Madrid a Allianz Arena

A yau Talata akwai gasar zakarun Turai da za’a gudanar zagayen kusa da karshe inda Bayern Munich zata karbi bakuncin Real Madrid a filin wasa na Allianz Arena, filin da za’a buga wasan karshe a ranar 19 ga watan Mayu.

Filin wasa na Allianz Arena, na Bayern Munich da za'a buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai a bana.
Filin wasa na Allianz Arena, na Bayern Munich da za'a buga wasan karshe a gasar Zakarun Turai a bana. REUTERS/Michaela Rehle
Talla

Dan wasan Bayern Munich Bastian Schweinsteiger yace zasu yi amfani da kwarin gwiwa a gida domin samun galabar Real Madrid.

Sai dai a wasanninsu na baya bayan nan Real Madrid ta lallasa Sportig Gijon ci 3-1, amma wasa tsakanin Bayern Munich da Mainz an tashi ne babu ci. Kuma maki 8 ne Borussia Dortmund taba Bayern a Tebur na Bundesliga.

Amma kuma a Tarihin haduwar kungiyoyin biyu, Bayern Munich ta samu galabar Real Madrid sau uku a shekarar 1976 da 1987 da 2001, Madrid kuma ta samu galabar Bayern sau daya a shekarar 2000.

A gobe Laraba ne Chelsea zata kara da Barcelona mai rike da kofin gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.