Isa ga babban shafi
Wasanni

Poland za ta tsananta bincike yayin wasan EURO 2012

Yayin da ake shirin fara gasar cin kofin nahiyar turai na wanna shekarar a watan yuni, da ake kira EURO 2012, daya daga cikin kasashen da za su dauki nauyin gasar, wato Poland, tace zata dawo da binciken mutanen da ke shiga kasar ba kakkautawa. A yau litinin, Ministan cikin gidan kasar ta Poland Jacek Cichocki yace za a fara wannan binciken ne daga ranar 4 ga watan yuni, kwanaki 4 kafin fara wasan ke nan.A shekarar 2007 kasar ta dakatar da irin wannan binciken, a lokacin da ta shiga tsarin nan na tafiyar mutane tsakanin kasashen Turai ba tare da tangarda ba, wanda ake kira Schengen. 

Alamar gasar Euro 2012.
Alamar gasar Euro 2012. DR
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.