Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Juventus ta lashe kofin Seria A, Manchester City na kusa da lashe Premier

Kungiyar Juventus ta lashe kofin Seria A bayan ta doke Cagliari a ranar Lahadi bayan AC Milan ta sha kashi a hannun Inter Milan, a Premer League kuma wasa daya ya rage a Manchester City ta lashe kofin gasar. Chelsea kuma ta lashe kofin FA bayan samu galabar Liverpool.

Wasu magoya bayan kungiyar Juventus mace da namiji rike da Tutar kungiyar suna sunbatar juna domin murnar lashe kofin Seria A bayan kammala wasa tsakanin Juventus da Cagliari
Wasu magoya bayan kungiyar Juventus mace da namiji rike da Tutar kungiyar suna sunbatar juna domin murnar lashe kofin Seria A bayan kammala wasa tsakanin Juventus da Cagliari REUTERS/Federico Tardito
Talla

Ingila

Manchester City ta samu galabar Newcastle ci 2-0, kuma Yaya Toure ne ya zirawa City kwallayenta a ragar Newcastle. Wasa daya ya rage a kammala Premier kuma City na gab da lashe kofin gasar bayan kwashe shekaru 44 ba tare da jin kamshin kofin ba.

Har yanzu dai Manchester City ce ke jagorancin Teburin Premier da yawan kwallaye, domin Manchester United ta doke Swansea ci 2-0.

City dai zata iya karbe kofin Premier hannun United idan ta lallasa QPR a ranar Lahadi. Manchester United kuma zata kara ne da Sunderland a wasan karshe.

A karshen mako dai wasa tsakanin Arsenal da Norwich an tashi ne ci 3-3, kuma Tottenham ta yi kunnen doki da Aston Villa.

A ranar Assabar ne kuma Cheslea ta lashe kofin FA bayan ta doke Liverpool ci 2-1 kafin su sake kece raini da juna a ranar Talata a Premier.

Spain

A La liga kuma ‘Yan wasan Barcelona sun yi bankwana da kocinsu Pep Gurdiola a wasan da Barcelona ta buga tsakaninta da Espanyol.

Barcelona ta lallasa Espanyol ci 4-0 kuma Lionel Messi ne ya zira kwallaye hudun a ragar Espanyol.

Yanzu kwallaye 72 ne Messi ya zira a raga.

Real Madrid kuma da ta lashe kofin la liga a bana ta doke Granada ci 2-1, kuma Cristiano Ronaldo shi ne ya zira kwallon shi ta 45 a raga, amma kwallaye 5 ne tsakanin shi da Messi.

Italia

A Seria A, Juventus ta lashe kofin gasar na 28 bayan AC Milan tasha kashi hannun Inter Milan ci 4-2, Juventus kuma ta lallasa Cagliari ci 2-0.

Juve ta samu nasarar lashe Seria A ne da tseren maki hudu tsakaninta da AC Milan saura wasa daya kacal a kammala Seria A .

Tun shekarar 2003 rabon Juve ta lashe kofin Seria A, kodayake an haramta wa Juve lashe kofin a kakar wasan 2005 da 2006 saboda sayar da wasa.
Jamus

A Bundesliga, kungiyar Cologne ta fice gasar bayan tasha kashi hannun Bayern Munich. A karshen mako kuma Borussia Dortmund da ta lashe kofin Bundesliga ta lallasa Frieburg ci 4-0.

Faransa

A Faransa PSG ta karbe ragamar jagorancin Tebur na French league daga hannun Montpellier bayan ta sha da kyar hannun Valenciennes. Amma a yau Litinin ne Montpellier zata kara da Rennes kafin ayi karon batta a karshen mako tsakanin PSG da Lille.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.