Isa ga babban shafi
Euro 2012

Ukraine ta lallasa Sweden, Ingila da Faransa sun yi kunnen doki

A gasar cin kofin Turai da ake gudanarwa a kasashe Poland da Ukraine, wasa tsakanin Ingila da Faransa an tashi ne kunnen doki ci 1-1. Amma Ukraine mai masaukin baki ta lallasa Sweden ci 2-1 a karawar farko da kasashen suka buga a rukunin D.

Dan wasan Ukraine  Andriy Shevchenko, a lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Sweden a gasar Euro 2012
Dan wasan Ukraine Andriy Shevchenko, a lokacin da yake murnar zira kwallo a ragar Sweden a gasar Euro 2012 REUTERS/Darren Staples
Talla

‘Yan wasan Manchester City guda biyu ne suka zira wa Faransa da Ingila kwallayensu a raga, inda Lescott ya fara zirawa Ingila kwallonta a raga daga bisani kuma abokin wasan shi a Man City Samir Nasri ya barke wa Faransa kwallonta a ragar Ingila.

A daya bangaren kuma Andriy Shevchenko ne ya zira kwallaye biyu daya ba Ukraine damar lallasa Sweden ci 2-1.

Ibrahimovic ne dai ya fara zira wa Sweden kwallonta a raga, kafin Andriy Shevchenko ya rama kwallon tare da sake zira kwallo ta biyu a ragar Sweden.

Yanzu haka dai Ukraine ce ke jagorancin Rukunin D wanda ke kunshi da Ingila da Faransa da Sweden.

Kocin Ingila Roy Hodgson da takwaran shi na Faransa Laurent Blanc dukkaninsu sun ce sun yaba da sakamakon wasan duk da cewa Faransa ta fi yawan taba kwallo, Ingila kuma suka yi kwance a gidansu.

A yau ne Rukunin A zasu sake fafatawa, inda Girka zata kara da Jamhuriyyar Czech, Rasha kuma ta kece raini da Poland mai masaukin baki.

A karawar Farko dai Rasha ta lallasa Jamhuriyyar Czech ci 4-1, Gika da Poland kuma suka yi kunnen doki.

Rahotanni daga Poland kuma na cewa ‘Yan wasan Spain sun ce zasu gabatar da kokensu ga hukumar EUFA game da kyawon filin wasan Gdansk Arena, bayan sun yi kunnen doki ci 1-1 da Italiya.

Wata majiya daga tagawar ‘Yan wasan ta shaidawa kamfanin Dilallacin labarun Faransa AFP cewa Xavi Hernandez da Cesc Fabregas sun koka game da kyawon filin wasan.

A filin wasan ne dai ‘Yan wasan Spain zasu sake karawa da Jamhuriyyar Ireland a ranar Alhamis sannan su sake karawa da Croatia a ranar 18 ga wata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.