Tottenham ta sallami Harry Redknapp
Kungiyar Tottenham a Ingila ta raba gari da kocinta Harry Redknapp bayan ya kwashe shekaru 4 yana aikin horar da ‘yan wasan kungiyar. A shekarar 2008 ne Redknapp ya fara aikin horar da ‘Yan wasan Tottenham bayan ya baro Portsmouth.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A bana Tottenham ta tsallake zuwa buga gasar zakarun Turai amma Chelsea ce ta haramtawa kungiyar bayan ta lashe kofin gasar a bana.
Redknapp dai ya taimakawa Tottenham lashe kofin FA, kuma ya taimakawa kungiyar zuwa zagayen Quarter Final a gasar zakarun Turai, tare da zuwa matsayi na hudu a Teburin Premier.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu