Isa ga babban shafi
Euro 2012

Makomar Laurent Blanc bayan Faransa ta fice Euro

Bayan ‘Yan wasan kasar Faransa sun huta a gida bayan ficewarsu a gasar Turai hannun Spain, yanzu haka hankalin kafafen yada labaran kasar ya karkata ne game da makomar Laurent Blanc a matsayin mai horar da ‘yan Faransa.

Laurent Blanc mai horar da 'Yan wasan Faransa
Laurent Blanc mai horar da 'Yan wasan Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Yanzu haka dai Laurent Blanc wanda yana cikin tawagar Faransa da suka lashe gasar cin kofin Duniya a shekarar 1998, kuma wanda ake wa kirari da sunan shugaba, babu wata sabuwar kwangila a hannun shi da Faransa.

Tuni kuma wasu Jaridu da dama suka ruwaito cewa kungiyar Tottenham Hotspur tana bukatar daukar Blanc a matsayin koci

Kodayake wasu Jaridun kasar sun ce akwai bukatar a ba Laurent blanc lokaci domin gina kungiyar Faransa, bayan ya taimakawa kungiyar Bordeaux lashe kofuna biyu a shekarar 2009.

Kamar yadda Jaridun suka ruwaito akwai tabbas daga shugaban hukumar kwallon kafar Faransa, Noel, zai sake sabunta kwangilar Laurent Blanc.

A ranar Assabar ne dai Spain ta yi waje da Faransa a gasar cin kofin Turai a zagayen Quarter final.

Kuma yanzu Spain da Jamus ne ake hasashen zasu iya buga wasan karshe a gasar Turai domin maimaita tarihi wasan karshe a shekarar 2008.

Amma hakan ba zai yiyuba har sai Spain ta Doke Portugal a gobe Laraba a zagayen kusa da karshe.

Kodayake a gasar cin kofin Duniya a Afrika ta Kudu Spain ta doke Portugal ci 1-0 a zagaye na biyu.

A wasan gobe dai karon batta ne tsakanin Cristiano Ronaldo da abokan wasan shi a Real Madrid da kuma abokan hamayyar shi a Barcelona.

A ranar Alhamis ne Jamus zata fafata da Italiya. Bayan Italiya ta kora Ingila gida, Jamus kuma ta lallasa Girka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.