Nadal da Murray da Serena sun haska a Wimbledon
Zakaran Roland Garros, Rafeal Nadal da Andy Murray na Birtaniya da Serena Williams ta Amurka da Petra Kvitova sun lashe wasanninsu na farko a gasar Wimbledon da ake gudanarwa a Birtaniya.
Wallafawa ranar:
Serena Willliams ‘Yar kasar Amurka tsohuwar jarumar gasar ta samu nasara ne akan Barbora ‘Yar kasar Jamhuriyyar Czech, bayan ‘Yar uwarta Venus Willaims ta fice gasar a zagayen farko.
Mai rike da kofin gasar Petra Kvitova ta sha da kyar ne hannun Amanmuradova ta Uzbekistan wanda ya bata damar tsallakewa zagaye na biyu.
Rafeal Nadal kuma ya doke Thomaz Bellucci ne dan kasar Brazil, Andy Murray kuma ya lallasa Nikolay Davydenko na Rasha.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu