Isa ga babban shafi
Olympic

Kenya tana neman lashe Zinari 12 a Olympic

Akwai zubin zaratan ‘Yan guje guje da tsalle tsalle a tawagar kasar Kenya da suka kai ziyara Birnin London, kuma mai horar da ‘yan wasan Juluis Kirwa yace Kenya za ta lashe Zinari 12 da wasu lambobin yabo 36.

David Rudisha dan tseren gudun kasar Kenya
David Rudisha dan tseren gudun kasar Kenya REUTERS/Brendan McDermid
Talla

Shekaru hudu da suka gabata a wasannin Olympic da aka gudanar a Beijing, Kasar Kenya ta lashe lambobin yabo 16, kodayake Shida daga cikinsu ne kawai Zinari.

Kasar Amurka ita ce kasa ta karshe da ta taba lashe Zinari 12 a wasannin guje guje da tsalle da aka gudanar da Atlanta shekarar 1996.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.