Isa ga babban shafi
Olympics

Bolt da Blake za su fafata a tseren mita 200

Usian Bolt na Jamica da Yohan Blake a yau Alhami ne za su sake fafatawa a tseren gudun mita 200 karo na karshe bayan sun tsallake zagayen kusa da karshe a jiya Laraba.

Usain Bolt yana gaisawa da Yohan Blake
Usain Bolt yana gaisawa da Yohan Blake REUTERS/Ivan Alvarado
Talla

Blake wanda ya lashe Azurfa a tseren gudun mita 100, a jiya shi ne ya zo na farko a tseren mita 200 cikin dakikoki 20.1. Sai kuma Bolt wanda ya lashe zinari a tseren mita 100 shi ne ya zo a matsayi na biyu cikin dakikoki 20.18.

A yau ne Bolt zai yi fatar lashe zinari kamar yadda ya lashe Zinari a tseren mita 100 da mita 200 a Beijing shekaru Hudu da suka gabata.

A tseren gudun mita 110 kuma na tsallakar karfe Aries Merrit ne na Amurka ya lashe Zinari a cikin dakikoki 12.92

Kazalika dan kasar Amurka kuma Jason Richardson ya lashe Azurfa a matsayin na biyu, sai kuma dan kasar Jamica Hansle ya karbi kyautar Tagulla.

A wasan jefa Mashi kuma dan kasar Kenya Julius Yego ya tsallake zuwa zagayen karshe bayan a jiya ya jefa matsin da ya kai nisan Mita 81.81.

Yegu wanda dan sanda ne shi ne karami cikin daukacin ‘Yan wasan da suka shiga gasar ta jefa mashin.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.