Isa ga babban shafi
Zakarun Turai

City ta fada tarko, Manchester da Chelsea da Arsenal za su iya sha.

Bayan fitar da rukunin kungiyoyin da za su kara da juna a gasar zakarun Turai, kungiyar Manchester City ta Ingila ta fada tarko domin an hada ta rukuni daya da Real Madrid da Ajax da Borussia Dortmund. Amma Chelsea za ta iya kare kofinta, inda Manchester da Arsenal za su iya huce kashin da suka sha a bara.

Allon rukunin kungiyoyin kwallon kafa da za su kara da juna a gasar zakarun Turai.
Allon rukunin kungiyoyin kwallon kafa da za su kara da juna a gasar zakarun Turai. REUTERS/Eric Gaillard
Talla

Rukunin A, an hada FC Porto Portugal ne da Dynamo Kiev ta Ukraine da Paris Saint-Germain Faransa da kuma Dinamo Zagreb Croatia.

Rukunin B kuma kungiyar Arsenal ta Ingila aka hada da Schalke 04 Jamus da Olympiacos ta Girka da kungiyar Montpellier Faransa.

A rukunin C, kungyar AC Milan ta Italia aka hada da Zenit Saint Petersburg ta Rasha da Anderlecht Belguim da Malaga Spain.

Ga alamu dai Manchester United da Chelsea za su yi dmurna ne bayan fitar da rukunin amma Manchester city sai ta yi da gaske domin an hada ta rukuni daya da real Madrid da Ajax da Borussia Dortmund.

Cheslea mai rike da kofin gasar bayan doke Bayern Munich a bara an hada ta wasa ne da Juventus da Shakhtar Donetsk, da kuma kungiyar Nordsjaelland da a karon farko za ta haska a gasar.

Wannan ne dai karon farko da Juventus za ta haska a gasar Zakarun Turai tun a kakar wasa ta 2009-10

Amma kuma Manchester United ta samu bagas ne a rukunin H domin an hada ta wasa ne da kugiyar FC Braga ta Portugal da Galatasaray ta Turkiya da kuma CFR-Cluj ta Romania.

A rukunin F, an hada Bayern Munich Jamus ne kungiyar Valencia ta Spain da kungiyar Lille ta Faransa da kuma BATE Borisov Belarus.

A rukunin G, kungiyar Barcelona ta Spain aka hada da kungiyar Benfica ta Portugal da Spartak Moscow Rasha da Celtic Scotland.

A ranar 18 da 19 ga watan satumba ne za’a fara fafata wa a gasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.