Isa ga babban shafi
Kwallon kafa

Marseille ta sha kashi, United da Bayern da Juve sun lashe wasanninsu

A gasar Seria A ta kasar Italia Francesco Totti ya zira kwallon shi ta 217 wanda hakan ke nuna dan wasan yana gab da kamo kafar dan kasar Sweden Gunnar Nordahl tsohon dan wasan AC Milan da Roma wanda ya zira kwallaye 225.

Dan wasan Roma Francesco Totti tare da abokan wasan shi.
Dan wasan Roma Francesco Totti tare da abokan wasan shi. REUTERS/Tony Gentile
Talla

Totti dai ya taimaka wa Roma doke Genoa ci 4-2.

Inter Milan kuma tana ci gaba ne da matsin lamba ga Juventus da ke jagorancin Tebur bayan ta doke Catania ci 2-0. Juventus kuma ta doke Napoli ci 2-0.

Tazarar Maki 4 ne Juve taba Inter a teburin Seria A. kuma a ranar uku ga watan Nuwamba ne Inter da Juventus za su kece raini da da juna.

Ingila

Sunderland da Newcatle sun yi kunnen doki ne ci 1-1. Haka ma QPR ta yi kunnen doki ne tsakaninta da Everton ci 1-1 amma Liverpool ta doke Reading ci 1-0.

Manchester Utd kuma ta casa Stoke ci 4-2, kuma Rooney da Van Persie da Welbeck su ne suka zira wa Manchester kwallayenta a raga.

Kungiyar Arsenal kuma ta sha kashi ne hannun Norwich 1-0 amma kungiyar Chelsea da ke jagorantar Teburin Premier ta lallasa Tottenham ci 4-2.

Jamus

A Bundesliga, Bayern Munich ta lashe wasanta na Takwas a jere da jere bayan ta casa Fortuna ci 5-0. Amma rikici ne ya barke a wasan Dortmund da Schalke 04 wanda har ya sa ‘Yan sandan Jamus suka cafke ‘Yan kallo kusan 200.

Schalke 04 ce dai ta lashe wasan ci 2-1 a filin wasa na Iduna Park.

Faransa

Kungiyar Marseille ta sha kashi hannun Troyes ci 1-0. Paris Saint Germain ce dai a saman teburin French League da yawan maki Uku bayan ta doke kungiyar Reims.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.