Serena da Venus Williams sun yi kira ga Matan Afrika su rungumi wasan Tennis
Fitattaun ‘Yan wasan Tennis na Duniya ‘yan kasar Amurka kuma ‘Yan uwan juna Serena da Venus Williams yanzu haka suna ziyara a Najeriya a karon farko domin domin yada fatawar ‘Yanci da kuma hanyoyin da za su taimaka ga ci gaban mata.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
A lokacin da suke ganawa da manama labarai Serena tace sun zo ne domin taimakawa Najeriya tare da ba mata musamman yara mata kanana kwarin gwiwa don sanar da su cewa suna iya cim ma duk wani guri da suka sa a gaba a rayuwa.
‘Yan wasan sun musanta zargin su ‘Yan asalin Najeriya ne kamar yadda ake yayatawa tsakanin ‘Yan Najeriya, ‘Yan wasan sun ce suna son Afrika amma su Amurkawa ne.
A yau Alhamis ne dai ‘Yan wasan za su kai ziyara makarantun mata, a gobe Juma’a kuma su kara da juna a birnin Lagos kafin su mika zuwa kasar Afrika ta Kudu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu