Isa ga babban shafi
Wasan kokuwa

An sace Zinaren ‘Yar wasan Kokuwan Faransa

Wasu daba a san ko su waye ba sun shiga gidan shahararriyar ‘Yar wasan Kokawar kasar Faransa, wato Lucie Decosse, inda suka yi awon gaba da Zinare guda uku da ta lashe a wasannin daban daban. A cewar ‘Yan sandan kasar Faransa, barayin sun shiga gidan Lucie, Yar shekaru 31, a Anguwar Thiais, dake birnin Paris.  

'Yar wasan Kokuwar Faransa, Lucie Decosse
'Yar wasan Kokuwar Faransa, Lucie Decosse Wikipedia
Talla

An yi satar ne a yayin da Lucie ta je kallon wasanni a Montepllier, wanda aka gudanar a tsakanin ranakun 23 da 25 a wannan watan na Nuwamba.
 

A wata hira da Lucie ta yi da Jaridar Sports Daily l’Equipe, ta ce ta yi mamaki ganin cewa barayin basu dauki wani abu ba sai zinaren guda uku.
 

Sai dai inda Allah ya yi wa Lucie gyadar dogo shi ne, ta fita da zinaren da ta lashe a gasar Olympics da aka gudanar a birnin London.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.